logo

HAUSA

Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Dandalin Tattaunawa Tsakanin JKS Da Jam'iyyun Siyasa Masu Bin Tsarin Markisanci

2022-07-28 21:27:02 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron dandalin tattaunawa tsakanin JKS da jam'iyyun siyasa masu bin tsarin markisanci a duniya.

Shugaba Xi ya ce, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin tana tsayawa kan hada muhimman ka'idojin markisanci da hakikanin yanayin kasar Sin da kyawawan al'adun gargajiyar kasar tare, da sa kaimi ga daidaita tsarin markisanci da yanayin kasar Sin yadda ya kamata, da neman ci gaba bisa tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin.

Xi ya jaddada cewa, a shirye JKS take ta karfafa mu'amala da tattaunawa da jam'iyyun siyasa masu bin tsarin markisanci a sauran kasashe, ta yadda tsarin markisanci zai nuna karfi na hakika a aikin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama. (Ibrahim)