logo

HAUSA

WHO: Kyandar biri ta fi kamari a Turai da sassan Amurka

2022-07-28 12:31:38 CMG Hausa

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, kyandar biri da ta barke a sassan duniya da dama, ta fi kamari a kasashen Turai da sassan Amurka.

Mr. Ghebreyesus, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Laraba, ya ce WHO ta samu rahoton harbuwar mutane sama da 18,000 da wannan annoba a kasashe 78 na duniya. Ya ce sama da kaso 70 bisa dari na masu dauke da cutar na a kasashen Turai ne, yayin da kaso 25 bisa dari ke sassan arewa da kudancin Amurka.

A ranar Asabar din da ta gabata ne WHO ta ayyana cutar kyandar biri a matsayin annobar lafiya ta gaggawa, wadda ya wajaba sassan kasa da kasa su mayar da hankali a kanta. Hukumar ta ayyana cutar a matsyin wadda ta kai matakin PHEIC, matsayin da shi ne mafi girma da WHOn ke ayyanawa ga duk wata cuta da ta barke. (Saminu Alhassan)