logo

HAUSA

Kasashen Afirka suna da hikimar zaben abokan hadin gwiwa da kansu

2022-07-27 20:02:45 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Afirka ita ce Afirka ta jama’ar Afirka, kuma kasashen Afirka tana da hikima da sanin ya kamata wajen zaben abokan hadin gwiwarta. Nuna goyon baya ga bunkasuwar Afirka, alhaki ne da kasa da kasa suka dauka tare.

Rahotanni sun bayyana cewa, kwamandan rundunar sojojin Amurka dake nahiyar Afirka Stephen Townsend ya bayyana a jiya cewa, yanayin tsaro a nahiyar Afirka yana da sarkakkiya, Sin da Rasha sun fi yin amfani da hanyoyin diplomasiyya, da tattalin arziki, da na soja, don kara fadada zuba jari da tasirinsu a nahiyar Afirka, da kuma amfani da taushin hali don neman sabuwar dangantakar abokantaka a nahiyar.

Game da wannan batu, Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, jami’an kasar Amurka sun nace kan ra’ayin yakin cacar baka tsakanin kasashe masu tsarin jari-hujja da masu bin tsarin gurguzu, da neman yin takara a tsakanin kungiyoyin kasa da kasa, da sanya ido kan harkokin sauran kasashen duniya, da mayar da hankali kan dakile tasirin wasu kasashe a Afirka, ayyukansu ko kadan bai dace ba.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, har kullum kasar Sin tana nuna kyakkyawar fata ga bunkasuwar nahiyar Afirka, kana taimako da goyon bayan da take baiwa Afirka wajen tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba ba zai ragu ba. Sin tana maraba da kasashen duniya ciki har da kasar Amurka, da su kara maida hankali wajen zuba jari ga nahiyar Afirka, kuma tana fatan dukkan abokan hulda, za su ci gaba da tabbatar da samun moriyar juna, da samun nasara tare, da bayar da gudummawar albarkatunsu da lokacinsu da karfinsu wajen biyan bukatun Afirka na samun ci gaba, da yin ayyukan alheri masu amfani, wadanda za su kai ga samar da hadin gwiwa mai inganci, ta yadda za a samu zaman lafiya da bunkasuwa a Afirka. (Zainab)