logo

HAUSA

Kamfanonin Faransa sun samu sakamako mai kyau yayin bikin baje kolin Hainan

2022-07-27 11:09:15 CMG Hausa

A halin yanzu, ana gudanar da bikin baje kolin hajoji na kasa da kasa na kasar Sin wato Hainan Expo karo na biyu, a birnin Haikou na lardin Hainan na kasar Sin. Wannan shi ne bikin baje koli mai taken “Hajoji masu kyau” na farko da kasar Sin ta kira, kuma, bikin baje koli na hajoji mafi girma da aka yi a yankin Asiya da Pasifik. Bikin ya kuma samu karbuwa sosai daga “tsoffin abokai”, wadanda suka halarci karo na farko, da kuma wasu sabbin abokai.

Bayan bikin baje kolin hajoji da aka yi a bara, yawan hajoji na wasu kamfanonin kasar Faransa da aka sayar, cikin shagunan ba harajin kwastan na lardin Hainan yana ci gaba da karuwa, don haka, a yanzu, akwai karin kamfanonin kasar Faransa da suka shigo tashar jiragen ruwa ta ’yancin ciniki ta lardin Hainan.

A wannan karo, a matsayin manyan baki a bikin, kamfanonin kasar Faransa sama da guda 50 sun halarci bikin, lamarin da ya sa kasar Faransa ta kasance ta biyu da kamfanonin ta suka fi halartar bikin bayan kasar Sin.

Jakadan kasar Faransa dake kasar Sin Laurent Bili ya bayyana cewa,“Kasar Sin tana da kasuwanni da yawa, kuma suna da kyau. A ganin ‘yan kasuwar kasashen duniya, akwai damammaki da dama cikin kasuwannin hajoji na kasar Sin. Kuma bikin baje koli na Hainan ya zama kyakkyawar alamar kara bude kofa ga waje da kasar Sin ta samar wa kasa da kasa.

A matsayin ta na babbar bakuwa a bana, kasar Faransa ta tura karin kamfanoni, da hajoji zuwa bikin, domin suna da imanin cewa, kasuwannin kasar Sin na da makoma mai haske sosai.” (Maryam)