logo

HAUSA

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sake mayar da martani game da yiwuwar ziyarar da Pelosi za ta kai yankin Taiwan

2022-07-25 21:01:26 CMG Hausa

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya jaddada a yau Litinin cewa, kasar Sin ta sha bayyana matukar damuwarta da ma matsayar ta ga bangaren Amurka, na nuna adawa da ziyarar da shugabar majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi za ta kai yankin Taiwan na kasar Sin.

Zhao Lijian ya nuna cewa, kasar Sin a shirye take. Idan har Amurka ta dage, to, ita ma kasar Sin za ta dauki kwararan matakai kuma masu karfi da suka dace, don kare ikon mallakar kasa da yankunanta, kuma ya kamata bangaren Amurka, ya dauki nauyin dukkan sakamakon da za su biyo baya.(Ibrahim)