logo

HAUSA

Yadda al’umma ke jin dadin yanayin tsaro a kasar Sin na kan gaba cikin shekaru 10 a jere

2022-07-25 14:25:05 CMG Hausa

Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin sun nuna cewa, ma’aunin yadda al’umma suke jin dadin yanayin tsaro a kasar, ya karu daga kaso 87.55 bisa dari na shekara ta 2012, zuwa kaso 98.62 bisa dari na shekara ta 2021. Kasa da kasa na ganin cewa, Sin daya ce daga cikin kasashe mafiya tsaro a duk fadin duniya. (Murtala Zhang)