logo

HAUSA

Amurka ita ce kasar da ke kan gaba wajen satar bayanai ta yanar gizo da yin leken asiri da sa ido kan sauran kasashe

2022-07-25 20:41:06 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kasar Amurka ita ce ta farko wajen satar bayanai ta yanar gizo da yin leken asiri da sa ido ga sauran kasashe a duniya.

Zhao Lijian ya bayyana cewa, hukumomin gwamnatin kasar Amurka da abin ya shafa, suna satar bayanan jama’a ta yanar gizo, amma ba a kiyaye su bisa doka. Kafofin watsa labaru na kasar Amurka da na kasa da kasa da dama, sun nuna rashin jin dadi ga wannan batu, kana sun nuna damuwa cewa, dalilin da ya sa ba a kiyaye tsarin sa ido ta yanar gizo a kasar Amurka a dogon lokaci ba, shi ne domin akwai matsala a cikin dokokin kasar dake shafar wannan batu. (Zainab)