logo

HAUSA

Kyakkyawar Dangantakar Da Ke Tsakanin Kasashen Sin Da Indonesiyya

2022-07-24 20:52:24 CMG Hausa

Shugaban kasar Indonesiyya Joko Widodo zai kawo ziyara a kasar Sin daga gobe Litinin 25 zuwa Talata 26 ga watan da muke ciki, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping ya yi masa. Shugaban ya zama na farko a duniya da zai kawo ziyara a kasar Sin, tun bayan gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, lamarin da ya nuna dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Indonesiyya bisa manyan tsare-tsare, kuma ziyarar za ta kara kuzari kan gina al'ummomin Sin da Indonesiyya mai makoma ta bai daya.

A shekarun baya, kasashen 2 sun rika zurfafa alakar abuta a tsakaninsu daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare, sakamakon jagorancin shugabanninsu da kuma kara azama da suke yi. A ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 2013, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar “gina hanyar siliki kan teku a karni na 21 tare ” karo na farko a yayin jawabinsa a majalisar dokokin Indonesiyya.

A shekarar 2015, yayin bikin tunawa da cika shekaru 60 da shirya taron Bandung, shugaban na kasar Sin ya gabatar da shawarwari guda 3 kan zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen Asiya da Afirka, habaka hadin kai a tsakanin kasashe masu tasowa da kara azama kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da masu sukuni, lamarin da ya kara sabon kuzari kan ruhun Bandung da kuma tabbatar da alkiblar samun kyakkyawar makomar Asiya da Afirka.

Layin dogo mai saurin tafiya da ake ginawa yanzu, zai hada birnin Jakarta, babban birnin Indonesiyya da birnin Bandung, birni na 4 mafi girma a kasar, tsayinsa zai kai kilomita 142 baki daya. Jirgin kasan zai rika gudun da zai kai kilomita 350 cikin awa guda. Layin dogon mai saurin tafiya na farko da kasar Sin ta gina baki daya a ketare, kana kuma zai zama na farko a Indonesiyya da ma yankin kudu maso gabashin Asiya.

A shekarar 2011, Indonesiyya, wadda ke rike da shugabancin karba-karba ta kungiyar ASEAN a wancan lokaci, ta gabatar da shawarar yarjejeniyar RCEP, wadda ta fara aiki a hukumance a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2022.

Shawarar “gina hanyar siliki kan teku a karni na 21 tare ”, ruhun Bandung, layin dogo mai saurin tafiya a tsakanin Jakarta da Bandung da yarjejeniyar RCEP, suna da muhimmanci matuka wajen raya hulda a tsakanin Sin da Indonesiyya a sabon zamani, su ne kuma ka’idojin yin mu’amala tsakanin kasashen 2 a nan gaba ba tare da wata matsala ba. (Tasallah Yuan)