logo

HAUSA

Sin ta yi na’am da sanya hannu kan yarjejeniyar fitar da hatsi ta tekun Bahar-Aswad

2022-07-23 17:43:26 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana gamsuwa, da sanya hannu kan yejejeniyar fitar da hatsi da takin zamani daga kasar Ukraine, zuwa kasuwannin duniya ta tekun bahar-Aswad, karkashin kulawar MDD.

Cikin wani sakon tiwita da ya wallafa, wakilin dindindin na Sin a MDD Zhang Jun, ya ce "Muna maraba da sanya hannu kan wannan yarjejeniya! Mataki ne mai matukar ma’ana".

Kafin hakan, a jiya Juma’a, kasashen Rasha da Ukraine, sun sanya hannu bi da bi, kan takardar amincewa da wannan yarjejeniya tsakanin su da kasar Türkiye da MDD, matakin da zai ba da damar ci gaba da safarar hatsi daga tashoshin ruwan Ukraine zuwa kasuwannin duniya.

Wata sanarwar da ofishin MDD ya fitar kan shafin yanar gizo, ta ce wannan mataki zai samar da ikon fitar da nau’o’in hatsi da takin zamani, daga muhimman tashoshin ruwan Odesa, da Chernomorsk da Yuzhny. (Saminu Alhassan)