logo

HAUSA

Tsarin aikin kandagarki da shawo kan annobar COVID-19 na majalissar gudanarwar kasar Sin: Rigakafin Covid-19 na da amfani

2022-07-23 17:58:36 CMG Hausa

A yau Asabar ne aka gudanar da taron ‘yan jarida, na tsarin hadin gwiwa ta kandagarki da shawo kan cutar COVID-19, wadda ke karkashin jagorancin majalissar gudanarwar kasar Sin, inda daraktan sashen lura da cututtuka masu yaduwa a cibiya ta biyar, ta babban asibitin rundunar sojojin ‘yantar da al’ummar kasar Sin Wang Fusheng, ya bayyana cewa, shaidun bincike masu yawa da aka samu a gida da waje, sun nuna yadda alluran rigakafin cutar COVID-19 suka yi matukar tasiri, wajen rage yiwuwar harbuwa da cutar. Kaza lika, Wang ya ce alluran rigakafin suna kuma dakile yiwuwar fuskantar tsananin cutar, da ma yiwuwar kisa da take yi.

Wannan dai ya dace da kudurin da hukumar kiwon lafiya ya duniya WHO ta amincewa, don gane da tasirin alluran rigakafin covid-19, wato bayar da kariya daga kamuwa da cutar, da tsanantar ta da kuma kisa. (Saminu Alhassan)