logo

HAUSA

Kamfanonin Sin da Jami’ar Uganda za su hada hannu wajen bunkasa basirar matasa

2022-07-22 11:09:08 CMG HAUSA

 

Kamfanonin kasar Sin dake Uganda, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da jami’ar Makerer ta kasar a kokarinsu na bayar da horan bunkasa basira da samar da aikin yi.

Kamfanonin karkashin inuwar cibiyar raya cinikayya ta kamfanonin kasar Sin a Uganda, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ce da jami’ar, a babban mazauninta dake Kampala, babban birnin kasar.

Shugaban zartaswa na jami’ar Makerere, Barnabas Nawangwe da wakilin cibiyar cinikayyar Zheng Biao ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

A cewar Zheng Biao, “ilimi shi ne tushen ci gaban kasa. A kasar Sin, mu kan ce idan aka ilmantar da matasa, to an ilmantar da kasa”. Ya kara da cewa, “za mu lalubo hanyoyin samun basirar gudanar da sana’o’i da fadada koyon makamar aiki ga dalibai da samar da ingantattun ma’aikata kuma masu basira, wadanda za su iya sajewa da sauyin tattalin arziki da yanayin zaman takewa.”  (Fa’iza Mustapha)