logo

HAUSA

Kasar Mali ta bukaci kakakin MINUSMA da ya bar kasar

2022-07-21 15:51:33 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin waje ta Mali, jiya Laraba ta bukaci kakakin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Mali wato MINUSMA, da ya bar kasar nan da sa’o’i 72, bayan da wani sako da aka wallafa a shafinsa na tiwita kan harkoki na diflomasiya ya kara daguwa al’amura a tsakanin bangarorin biyu.

A makon da ya gabata ne Mali ta sanar da dakatar da duk wasu sabbin ayyukan wanzar da zaman lafiya na tawagar MINUSMA zuwa wani lokaci saboda dalilai na tsaro. Wannan sanarwa na zuwa ne, kwanaki kadan, bayan da hukumomin Mali suka kama sojojin 49 daga Cote d'Ivoire, bisa tuhumar da laifin shiga kasar ba tare da izini ba.

A cikin wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Mali ta bayar a ranar Laraba, ta zargi kakakin tawagar MINUSMA Olivier Salgado, da yin wasu rubuce-rubuce a shafin sada zumunta na tiwita "Ba tare da wata shaida ba", cewa an sanar da hukumomin Mali game da zuwan wadancan sojoji 49.(Safiyah Ma)