logo

HAUSA

Jami’ar MDD ta yi kira da a sauya tunani domin cimma manufofin ci gaban Afirka

2022-07-21 10:19:21 CMG Hausa

Mataimakiyar babban sakataren MDD, Amina Mohammed ta bayyana cewa, har yanzu za a iya cimma burin da ake da shi na raya nahiyar Afirka, kuma tabbatar da hakan, yana bukatar sauya tunani tare da magance rikici zuwa ga samar da damammaki.

Amina Mohammed, ta shaida wa babban taron manyan jami’ai na musamman dake tattauna batun ci gaba mai dorewa na Afirka, bisa taken "Afirka da muke so: Sake tabbatar da ci gaban Afirka a matsayin tsarin da MDD ke baiwa fifiko”, cewar ita ma MDD tana da ra'ayin "Afirka da muke so" kamar yadda aka tsara a cikin ajandar raya nahiyar ta kungiyar tarayyar Afirka nan da shekarar 2063, da tabbatar da wannan buri, ta hanyar ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030.

Da take jawabi a madadin babban sakataren MDD Antonio Guterres, Amina Mohammed ta ce, tattaunawar ta samar da wani tsari na duniya ga kasashen Afirka mambobin majalisar, da ita kanta MDD da abokan hadin gwiwa, don raba ci gaban da aka samu, tare da tabbatar da cewa, "karfafa wannan hangen nesa, shi ne abin da muka dora muhimmanci a kansa baki daya."

Ta yi nuni da cewa, ci gaban Afirka na cikin hadari, sakamakon rikice-rikice guda uku da ake fama da su a halin yanzu, wato annobar COVID-19, da matsalar sauyin yanayi, da kuma yakin Ukraine. (Ibrahim)