logo

HAUSA

Yawan hatsin da aka samu a yanayin zafi a Sin ya kai matsayin koli a tarihi

2022-07-20 14:46:11 CMG Hausa

Ma’aikatar raya ayyukan gona da karkara ta kasar Sin, ta bayyana a yau cewa, tattalin arzikin bangaren ayyukan gona da na kauyuka, ya ci gaba da bunkasa cikin kwanciyar hankali a rabin farkon bana, haka kuma yawan hatsin da ake samarwa ya kai matsayin koli a tarihi, inda ya kasance tushen girbin hatsi mai yawa a bana.

Shugaban sashen kula da tsare-tsare na ma’aikatar, Zeng Yande ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira da misalin karfe 10 na safiyar yau, domin yi bayani kan yanayin tattalin arzikin ayyukan gona da na kauyuka, a rabin farkon shekarar 2022.

Zeng Yande ya kara da cewa, yanayin kasuwa na cikin kwanciyar hankali, kuma nasarorin da aka samu na rage radadin talauci na ci gaba da karfafa, inda ake ci gaba da inganta ayyukan gona.

Bugu da kari, ya ce bunkasar tattalin arzikin ayyukan gona a rabin farko na bana, ya tallafa wajen daidaita farashin kayayyaki da rayuwar al’umma da kuma ci gaban tattalin arzikin kasar. (Safiyah Ma)