logo

HAUSA

Guterres ya yi kira da a dauki mataki don girmama kyawawan halayen Nelson Mandela

2022-07-19 09:59:58 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana marigayi Nelson Mandela, a matsayin "mai da'a”. Yana mai kira da a girmama kyawawan halayen da tsohon shugaban Afirka ta Kudun ya bari, ta hanyar daukar matakai.

Guterres ya ce, duniyarmu a yau tana fama da yaki, da mamayar abubuwa na gaggawa, da nuna wariyar launin fata, da kyama, da talauci, da rashin daidaito, da kuma barazanar matsalar sauyin yanayi. Don haka, ya ce, ya dace mu samu fata, ga misalan da Nelson Mandela ya nuna, da kokarin koyi da hangen nesansa.

Jami’in na MDD ya kuma bayyana cewa, hanya mafi dacewa wajen girmama abubuwan da Mandela ya bari, ita ce ta daukar matakai.

Guterres ya ce, ta hanyar fitowa fili wajen nuna adawa da kiyayya da tsayawa tsayin daka don kare hakkin dan adam. Ta hanyar rungumar daukacin bil-Adama na bai daya, masu wadata daga dukkan bangarori, daidato a fannin martaba, hadin kai wajen daukar mataki. Haka kuma hada kai ta hanyar mayar da duniyarmu ta kasance mai adalci, da tausayi, da wadata, da dorewa ga kowa. (Ibrahim)