logo

HAUSA

Kasashen duniya sun san wadanda ke haddasa matsalar abinci a duniya

2022-07-19 20:22:10 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata cewa, yana fatan Amurka za ta yi tunani da gaske, kan rawar maras kyau da take takawa game da matsalar karancin abinci a duniya, kuma ta kauracewa yin zarge-zarge marasa tushe da bata sunan kasar Sin.

Rahotanni sun bayyana cewa, a baya shugabar hukumar samar da ci gaba ta kasa da kasa dake Amurka wato USAID a takaice, Samantha Power, ta ce takunkumin da kasar Sin ta dora game da cinikin taki, da kuma tara kayan abinci, na daya daga cikin dalilan da suka haddasa bala'in yunwa a yankin kahon Afirka.

Game da hakan, kakakin ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa, don haka ba ta da nauyin shiga ayyukan Taimakon Ci gaban Hukuma, wato ODA a takaice. Duk da haka, a matsayinta na kasa ta biyu mafi girma wajen bayar da kudin MDD, kuma babbar kasa mai daukar nauyi, kasar Sin tana taka rawar gani, wajen yin hadin gwiwa a fannin raya kasa da kasa, tare da samar da dimbin albarkatun raya kasa ga hukumomin raya kasa na MDD, ciki har da hukumar abinci da aikin gona ta MDD, ta yadda ta ba da gudummawa mai yakini, don tabbatar da wadatar abinci a duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)