logo

HAUSA

Yawan tashar sadarwa ta 5G da Sin ta gina ya kai kusan miliyan 2

2022-07-19 14:23:51 CMG HAUSA

Jami’in hukumar kula da aikin sadarwar ta ma’aikatar kula da masana’antu da aikin sadarwa ta kasar Sin Wang Peng ya bayyana a gun taron manema labarai da aka yi yau Talata cewa, yawan tashoshin sadarwar 5G da Sin ta gina, sun kai miliyan 1 da dubu 854, daga cikinsu karin sabbin tasoshin da aka gina a watannin Afrilu da Mayu da Yuni ya kai kusan dubu 300, matakin da ya tabbatar da cewa, duk wata gunduma na iya kama da sakwani na 5G, yayin da kowane kauye ke iya kama layin Intanet.

Raya manyan ababen sadarwa, ya dasa harsashe wajen bunkasa tattalin arziki na zamani. A watanni 6 na farko a bana, an samu saurin bunkasar yin sayayya a intanet da ba da ilmi da jiyya ta intanet, kana an raya sha’anin yanar gizo ba tare da wata tangarda ba. Ya zuwa karshen watan Yunin bana, jimillar kudaden shigar da aka samu a fannonin kera kayan laturoni na zamani da samar da manhajoji da aikin sadarwa da kuma Intanet ta wuce kudin Sin Yuan triliyan 10. (Amina Xu)