logo

HAUSA

Ma’aikatar wajen Sin: Kifar da gwamnatocin kasashen waje ya zamewa Amurka jini da tsoka

2022-07-18 21:08:16 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce burin Amurka na kifar da gwamnatocin kasashen waje, domin biyan bukatar kashin kai, ya zama ruwan dare cikin manufofin wajen kasar.

A baya bayan nan, tsohon mai taimakawa shugaban Amurka game da harkokin tsaro John Bolton, ya furta da bakin sa cewa, ya taimakawa gwamnatin Amurka, wajen hambarar da gwamnatocin wasu kasashen duniya. A yayin taron manema labarai da ya gudana a Litinin din nan, lokacin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa mai nasaba da hakan, Wang Wenbin ya ce, "Cikin shekaru da suka gabata, Amurka ta haifar da tashe tashen hankula da dama a yankunan Latin Amurka, ta kuma tsoma hannu cikin juyin juya halin da ya kifar da wasu gwamnatocin kasashen larabawa, da wasu rigingimu a gabas ta tsakiya. Kaza lika Amurka ta rura wutar juyin juya hali a wasu kasashen Turai da Asiya.

A wasu lokacin ma, an ga manyan jami’an Amurka na shigewa gaba wajen goyon bayan ‘yan adawa a wasu kasashe, domin haifar da fito-na-fito na siyasa. Bugu da kari, kalaman Mr. Bolton sun kara shaida manufar kasar sa, ta tabbatar da 'mulkin kasa da kasa bisa ka’idoji', wanda ‘yan siyasar Amurkan ke amfani da shi don tabbatarwa Amurka ikon tsoma baki cikin al’amuran sauran kasashen duniya. Wannan salon na mulki bisa ka’idoji, shi ne Mr. Bolton, da sauran masu ra’ayi irin na sa suke son tabbatarwa, duk da cewa hakan bai samu karbuwa daga sauran al’ummun duniya ba.  (Saminu)