logo

HAUSA

Kafofin yada labaran Syria: Sojojin Amurka sun mika man da aka sace a arewa maso gabashin Syria

2022-07-17 17:03:16 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labaran Syria ya rawaito cewa, sojojin Amurka sun yi jigilar man da aka sace daga arewa maso gabashin kasar, zuwa arewacin Iraki ta kan iyaka.

Kamfanin dillancin labaran Syria ya ruwaito majiyar kasar na cewa, motoci 40 da suka hada da tankunan dakon man da aka sace da kuma manyan motoci dauke da kayan sojoji, sun tafi arewacin Iraki ne bisa rakiyar wasu motocin sulke na Amurka.

A shekarun baya-bayan nan dai, gwamnatin Syria ta sha zargin sojojin Amurka da sata tare da tura mai daga arewa maso gabashin kasar.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)