logo

HAUSA

FT: Amurka ba ta yi kama da kasa mai ci gaba ba

2022-07-17 17:02:12 CMG Hausa

Jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya, ta buga wata kasida a baya-bayan nan tana mai cewa, kasadar siyasa a Amurka na karuwa yanzu, kana rarrabuwar kawuna na kara zurfi, kuma amincewar jama'a ga gwamnati ta kai wani matsayi mafi karanci, kana Amurka ba ta kama da wata kasa mai ci gaban tattalin arziki.

Kasidar mai taken “Shin Amurka Na Zama Kasuwa Mai Tasowa Ce?” ta ce, tun bayan barkewar matsalar kudi a shekarar 2008, hukunce-hukuncen da jam’iyyu biyu na majalisar dokokin kasar suka yanke, ciki har da ceto bankuna maimakon ceto iyalai da rage harajin kamfanoni, sun haifar da raguwar amincewar Amurkawa ga hukumomin gwamnati. A cewar wani binciken jin ra’ayin jama’a na baya-bayan nan da kamfanin ba da shawara na Gallup na kasar ya yi, amincewar da Amurkawa ke da shi ga hukumomin gwamnati a halin yanzu, ya kai matsayin mafi karanci a tarihi.

Kasidar ta ce, a yanzu Amurka na fuskantar matsaloli kamar karuwar harbe-harbe a ko'ina da hauhawar farashin kayayyaki cikin sauri, kana taron sauraron shaidu kan lamarin tarzomar ‘yan majalisar dokokin Amurka da aka watsa ta talabijin, ya baiwa kowane dalibi damar ganin cewa tashin hankali irin wannan na iya faruwa a Amurka. Wadannan sun sa wasu masu zuba jari fara zargin cewa, idan aka yi la’akari da hadarin siyasa da rashin tabbas, "ko Amurka ta fara zama kasuwa mai tasowa maimakon kasa mai ci gaba."  (Mai fassara: Bilkisu Xin)