logo

HAUSA

Shugabanni sun lashi takobin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya

2022-07-17 16:38:26 CMG Hausa

Taron tsaro da ci gaba na Jeddah, ya jaddada muhimmancin daukar matakan da suka wajaba, na kare tsaro da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ne ya ruwaito sanarwar bayan taron na jiya, wanda kasar Saudiyya ta karbi bakuncinsa.

Taron ya samu halartar shugabannin kasashen majalisar hadin gwiwa ta yankin Gulf da kasashen Masar da Iraqi da Jordan da Amurka.

Taron ya kuma nazarci kalubalen da duniya da yankin ke fuskanta, yayin da shugabannin suka nanata kudurinsu na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.

Sun kuma bayyana goyon bayansu ga tabbatar da ganin babu makaman kare dangi a yankin Gulf.

Shugaban Amurka Joe Biden, ya halarci taron ne a ranar karshe ta ziyararsa a yankin Gabas ta Tsakiya, wadda ta kunshi ziyartar Isra’ila da yankin yammacin kogin Jordan. (Fa’iza Mustapha)