logo

HAUSA

Masana: Raguwar darajar kudin Amurka za ta haifar da babbar illa ga tattalin arzikin duniya

2022-07-16 16:13:51 CMG Hausa

Masanan tattalin arziki da dama na kasa da kasa sun bayyana cewa, yanzu haka, darajar kudin Amurka ta ragu da babban mataki, don haka asusun ko ta kwana na tarayyar Amurka ya fitar da manufar kara kudin ruwa, abubuwan da suke ganin za su haifar da babbar illa ga tattalin arzikin duniya.

Masanin ilmin siyasa da tattalin arziki na jami’ar Sao Paulo ta kasar Brazil, Marcos Pires ya bayyana cewa, matakin kara kudin ruwa na asusun ko ta kwana na tarayyar Amurka, zai haifar da tabarbarewar tattalin arzikin duniya, musamman ma na kasashen da suke da nasaba da tsarin hada-hadar kudi ta Amurka. Ya ce a halin yanzu, kasar Brazil tana fama da matsalar rashin aikin yi mai tsanani, har al’ummun kasar kusan miliyan 31 ba sa iya samun isasshen abinci a ko wace rana.

A nasa bangaren, masanin tattalin arziki na kasar Singapore, Ye Xiuliang, ya ce, raguwar darajar kudin Amurka za ta kawo babbar matsala ga kasashen dake fama da talauci, kuma al’ummomin kasashen duniya za su sha wahala sakamakon bahaguwar manufar ta Amurka.

Shi ma mataimakin darektan hukumar nazarin ilmi ta ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, Zhang Jianping cewa ya yi, idan Amurka ta aiwatar da manufar kara kudin ruwa, tabbas za ta kawo babbar matsala ga tattalin arzikin kasashe masu tasowa da kasashen da suke samun ci gaba cikin sauri. (Jamila)