logo

HAUSA

Sin ta samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 6.5 a biranen kasar a rabin farko na bana

2022-07-15 19:28:49 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Sin, ta samar da guraben ayyukan yi na birane da yawan su ya kai sama da miliyan 6.54, cikin watanni shida na farkon shekarar bana. Alkaluman hukuma sun nuna cewa, adadin ya kai kaso 59 bisa dari, na burin da kasar ta sanya gaba a cikin shekarar.

Ma’aikatar kula da albarkatun al’umma da jin dadin jama’a ta kasar Sin, ta ce yanayin samar da ayyukan yi a kasar ya ci gaba da kasancewa cikin yanayi na daidaito. (Saminu)