logo

HAUSA

Xi ya ziyarci birnin Shihezi na jihar Xinjiang

2022-07-15 13:30:23 CMG Hausa

 

Xi Jinping, babban sakatare na kwamitin koli na JKS, ya ziyarci birnin Shihezi a yammacin Larabar nan, yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Xi ya ziyarci gidan adana kayan tarihi na ma’aikatan dake aikin samar da kayayyaki da kare kan iyakar Xinjiang (XPCC) da kuma wani bangare da ke karkashin sashen XPCC.(Ibrahim Yaya)