logo

HAUSA

Yang Xiaodu ya yi kira ga mambobin BRICS da su samar da tsarin gudanar da yaki da cin hanci da rashawa

2022-07-14 10:37:25 CMG Hausa

 

Shugaban hukumar ayyukan sa ido ta kasar Sin Yang Xiaodu, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar BRICS, da su yi hadin gwiwa wajen kare tsarin cudanyar sassan kasa da kasa, su kuma samar da tsarin gudanar da yaki da cin hanci da rashawa.

Yang Xiaodu, ya yi wannan tsokaci ne a jiya Laraba, yayin da yake tsokaci ga taron tattauna batutuwan da suka jibanci cin hanci da rashawa, na ministocin kasashen kungiyar ta BRICS, wanda ya gudana ta yanar gizo.

Yang ya ce yaki da cin hanci aiki ne na bai daya ga dukkanin kasashen duniya, don haka akwai bukatar kasashe mambobin BRICS su gina tsarin amincewa a siyasance, tare da aiwatar da hadin gwiwar BRICS na kalubalantar ayyukan cin hanci da rashawa.

Jami’in ya kara da cewa, ya kamata kasashe mambobin kungiyar BRICS su zurfafa koyi da juna, domin inganta tsarin gudanarwa a fannin yaki da cin hanci, kana su yi aiki tare wajen samar da tsaftacaccen yanayin gudanar da hada hadar kasuwanci.

Yang ya ce "Ya kamata mu goyi bayan cudanyar sassa daban daban, mu yi aiki tare don gina tsarin adalci na yaki da rashawa, kana mu kara zurfafa gudummawar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama, da ci gaban duniya baki daya".  (Saminu)