logo

HAUSA

Mekka: Jiragen Kasan Kasar Sin Sun Kammala Aikin jigilar Alhazan Bana

2022-07-13 11:01:50 CMG Hausa

Jiya ne, kamfanin dake aikin shimfida hanyar dogo na kasar Sin wato CRCC ya kammala aikin dauko alhazan bana dake Mekka na kasar Saudiyya cikin nasara.

Zhang Long, darektan kula da tafiyar da jiragen kasa a Mekka na kamfanin CRCC ya bayyana cewa, sakamakon yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, ya sa sai bayan shekaru biyu jiragen kasan da ke zirga-zirga a cikin Mekka, suka sake jigilar alhazai. A bana jiragen kasan da ke zirga-zirga a Mekka guda 2,228 sun shafe awoyi 158 suna jigilar alhazai daga ranar 6 zuwa 12 ga wata, inda suka yi jigilar alhazai fiye da miliyan 1 da dubu 290.

Tsawon hanyar jirgin kasa dake Mekka ya kai kilomita 18.25, tare da tasoshi guda 9. Jirgin kasan yana tafiya a tsakanin yankunan dake gudanar da aikin hajji guda 3. Haka kuma jiragen na jigilar alhazai kusan dubu 72 a cikin sa’a guda. Kamfanin CRCC ne ya shimfida layin dogon, wanda aka fara aiki da shi a ranar 13 ga watan Nuwamban shekarar 2010 a hukumance. Layin dogon ya zama na farko a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda kamfanin kasar Sin ya shimfida, kana na farko a kasar Saudiyya.

Ya zuwa wannan shekara, kamfanin CRCC ya kammala jigilar alhazai sau 8, inda yawan zirga-zirgar alhazan ya wuce miliyan 20 baki daya. Kamfanin ya kuma samu yabo daga masu kula da hanyar dogon da fasinjoji, ya kuma taimaka wajen horas da kwararru masu fasahar layin dogo, da harkokin gudanarwa a kasar Saudiyya.(Tasallah Yuan)