logo

HAUSA

Tsarin cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje na da juriya

2022-07-13 20:46:08 CMG Hausa

Jimillar darajar kayayyakin shige da fice a kasar Sin cikin rabin farko na bana, ya kai yuan triliyan 19.8, kwatankwacin dala triliyan 2.94, wanda kuma ya karu da kaso 9.4 a kan na bara.

Cinikin Sin da kasashen ketare ya iya jurewa mummunan tasirin annobar COVID-19, saboda yadda sassan duniya ke ci gaba da bukatar kayayyakin da aka samar a kasar Sin.

Bisa yadda kasar Sin ta samu nasarar dawowar harkokin aiki da na samar da kayayyaki daki-daki, ana sa ran cinikayya tsakaninta da kasashen ketare zai ci gaba da bunkasa da kuma ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)