logo

HAUSA

Shugabannin Rasha da Turkiyya sun tattauna kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu da kuma yanayin Ukraine

2022-07-12 14:43:10 CMG HAUSA

 

Jiya ne, shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna ta waya tare da takwaransa na kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, game da karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu da yanayin da ake ciki a Ukraine da sauran abubuwa.

Shafin intanet na fadar Kremlin ya bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu sun mai da hankali, kan ci gaba da karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu, da suka hada da daukar matakan inganta harkokin tattalin arziki da cinikayya da habaka jimilar cinikayyar sassan biyu da amfani da albarkatu da ci gaba da samar da makamashin Rasha ba tare da katsewa ba. (Safiyah Ma)