logo

HAUSA

Sin da Pakistan na karfafa hadin kai a tsakaninsu a bangarori daban-daban

2022-07-11 11:26:29 CMG HAUSA

Ran 21 ga watan Afrilu na shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi mai taken “Kafa kyakkyawar makomar Sin da Pakistan ta bai daya, da bude sabon babin hadin kansu”, matakin da ya daga matsayin huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa dangantakar hadin kai a duk fannoni bisa manyan tsare-tsare. A cikin shekaru 7 da suka gabata, Sin da Pakistan, sun gudanar da matakan zurfafa hadin kan su a duk fannoni.

An fara aiwatar da aikin tura wutar lantarki tsakanin Matiari da Lahore, karkashin tsarin hadin gwiwar raya tattalin arziki na Sin da Pakistan a watan Satumba na shekarar 2021. A matsayin aiki mafi muhimmanci wajen jigilar wutar lantarki tsakanin kudu da arewacin kasar, wannan aiki ya daga karfin jigilar. Injiniya na tashar Matiari Mir Arslan Ali ya bayyana cewa, amfani da wannan aiki na alamanta cewa, Pakistan na maraba da wani sabon karni na jigilar wutar lantarki. Ya ce:

“Wannan aiki ya kasance irin sa na farko a fannin jigilar wutar lantarki mai karfi a kasar, abin da alamta ci gaban kimiyya da fasaha a duniya a wannan fanni, kuma kammala aikin gina tsarin ya daga matsayin kasar a fannin fasahar wutar lantarki mai karfi, da karfin sarrafa tsarin wutar lantarki. Ina alfaharin zama injiniya a wannan fanni, duba da cewa kasar mu tana da karancin samun irin wannan dama. Ban da wannan kuma, ina koyon fasaha ta zamani a wannan fanni.”

Bisa labarin da aka bayar, a karkashin tsarin hadin gwiwar raya tattalin arziki na Sin da Pakistan, bangarorin biyu sun kafa tsare-tsarensu na hangen nesa, da tashar jirgin ruwa ta Gwadar, da makamashi, da manyan ababen more rayuwa a bangaren zirga-zirga, da masana’antu, da zaman rayuwar al’umma, da kimiyya da fasaha, da hadin gwiwa a fannin tsaro da hadin kan kasa da kasa, da fasahar sadarwa da dai sauransu har bangarori 11, hakan ya sa an habaka abubuwan da za a yi karkashin wannan nagartaccen tsari, wanda ke kara samun ci gaba mai inganci. (Amina Xu)