logo

HAUSA

Manufar ziyarar Joe Biden a Gabas ta Tsakiya na da sarkakiya

2022-07-11 21:15:49 CMG Hausa

A cikin wannan mako ne shugaban Amurka Joe Biden, zai ziyarci Isra’ila da yankin kogin Jordan da kasar Saudiyya. Cikin wata mukalarsa da jaridar Washington Post ta wallafa, Joe Biden ya yi ikirarin cewa, ziyarar tana da muhimmanci ga tsaron Amurka, yana mai jaddada neman nasara kan abun da ya kira “takara da kasar Sin”.

Bisa la’akari da yadda Amurka ke yayata kungiyar tsaro ta NATO a duniya, ta sanya yankin Gabas ta Tsakiya cikin batutuwanta na siyasa. Sai dai, ko manufar ziyarar ita ce, kyautata hulda da kawayen Amurka ko kuma neman goyon bayan Gabas ta Tsakiya wajen adawa da kasar Sin, abu ne mai wuya hakar Joe Biden ta cimma ruwa, domin babu wata kasa da ta shirya watsar da muradunta domin Amurka ta samu karfin danniya. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)