logo

HAUSA

Wang Yi ya jaddada bukatar aiwatar da matakan gudanar da cudanyar sassa daban daban a zahiri

2022-07-10 20:41:42 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar G20, da su nacewa aiwatar da matakan gudanar da cudanyar sassa daban daban a zahiri, domin wanzar da zaman lafiya, da ingiza ci gaban bai daya a duniya baki daya.

Wang, ya yi wannan tsokaci ne a ranar Juma’a, lokacin da yake halartar taron ministocin wajen kasashe mambobin G20 a Bali na kasar Indonesia.

Kungiyar G20 dandali ne na kasashe 19, masu samun saurin bunkasar tattalin arziki da tarayyar Turai EU. (Saminu)