logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Warware Sabanin Siyasa A Yammacin Afirka Da Sahel Ta Hanyar Shawarwari

2022-07-09 15:58:24 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, yi kira da a gudanar da tattaunawa domin warware sabanin siyasa da ake fama da shi a yammacin Afirka da yankin Sahel.

Da yake jawabi a yayin zaman kwamitin sulhu na MDD game da ofishin MDD mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel (UNOWAS) a ranar Alhamis din da ta gabata, Dai Bing, ya ce tilas ne a kara kaimi "don tsayawa tsayin daka kan turba madaidaiciya wajen warware bambance-bambancen siyasa a yammacin Afirka da Sahel ta hanyar tattaunawa."

Da yake karin haske kan zabuka a kasashen Najeriya da Senegal da Saliyo da Benin da Togo da dai sauransu kuwa, Dai ya ce, ya kamata kasashen duniya su mutunta 'yancin kai da shugabancin kasashen yankin, su kuma ba su goyon baya wajen bin hanyoyin ci gaba da suka dace da yanayin kasashensu, tare da tallafawa bangarorin da abin ya shafa, wajen warware sabanin ra'ayi ta hanyar tattaunawa.

A baya-bayan nan ne dai, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS, ta gudanar da taron koli, inda ta yanke wasu muhimman shawarwari kamar dage takunkuman da aka sanyawa kasar Mali.

Jakadan kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan Afirka wajen lalubo hanyoyin warware matsalolinsu da kansu, kana tana goyon bayan kungiyar ECOWAS, wajen ci gaba da yin shawarwari da kasashen da ke fuskantar sauyin siyasa, tare da ciyar da harkokin siyasa gaba ta hanyar da ta dace.(Ibrahim)