logo

HAUSA

An kira taron ministocin harkokin waje na G20

2022-07-08 13:51:26 CMG Hausa

Yau Jumma’a, aka bude taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 a tsibirin Bali na kasar Indonesiya. Taken taron shi ne "Hada kai don gina duniya mai zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata".

Tun daga ranar 7 ga wata, ministocin harkokin wajen kasashen G20 suka fara shawarwari a tsakaninsu, daya bayan daya.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)