logo

HAUSA

Tsohon firayim ministan Japan ya mutu bayan harbinsa da aka yi a Nara

2022-07-08 20:14:18 CMG Hausa

 

            

Rahotanni na cewa, wani dan bindiga ya harbe tsohon firaministan kasar Japan Shinzo Abe, yayin da yake gabatar da jawabi a birnin Nara da ke yammacin kasar, a lokacin da yake yakin neman zaben 'yan majalisar dattawan kasar da za a gudanar ranar Lahadi.

Abe, mai shekaru 67 da haihuwa, ya fadi kasa kuma an ga yana zubar da jini, bayan da aka harbe shi a baya da karfe 11 da rabi na safe agogon wurin, lokacin da yake jawabi a gaban tashar jirgin kasa ta Kintetsu ta Yamato-Saidaiji, kamar yadda 'yan sanda da jami'an kashe gobara suka bayyana.

A cewar ‘yan sanda da jami’an agajin gaggawa na yankin, an garzaya da shi zuwa wani asibiti da ke kusa, kuma bai nuna alamun zai rayu ba.

Tsohon firaministan ya rasu ne da misalin karfe 5 da mintuna na yamma agogon wurin, kamar yadda asibitin da aka kai karbar Abe ya shaida wa taron manema labarai yau da rana.(Ibrahim)