logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen Sin da Saudiya sun gana tare da shan alwashin zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashensu

2022-07-08 21:14:22 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Saudiya yarima Faisal bin Farhan Al Saud a tsibirin Bali na kasar Indonesia, inda ya bayyana aniyar kasar Sin ta yin hadin gwiwa da inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Yayin ganawarsa da Faisal a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20 da aka gudanar a tsibirn Bali na kasar Indonesia, Wang Yi ya bayyana cewa, hakika kasarsa tana goyon bayan kasar Saudiyya wajen kare ikon mulkin kasa, tsaro da zaman lafiya, kuma tana adawa da duk wani nau’i na tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidanta.

Wang Yi ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan Saudiyya wajen taka muhimmiyar rawarta a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A nasa bangaren kuwa, Yarima Faisal ya ce, kasar Saudiyya tana ci gaba da tsayawa tsayin daka, wajen martaba manufar “Sin daya tak a duniya”, kuma kullum tana adawa kan duk wani tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan kasar Sin, yana mai cewa, a shirye kasar Saudiyya take ta zurfafa hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasar Sin.(Ibrahim)