logo

HAUSA

Kasashen Afirka za su fara hada-hadar cinikayyar hannayen jari tsakanin su

2022-07-07 10:11:49 CMG Hausa

Tun daga watan Oktoban bana, masu hada hadar hannayen jari a kasashen nahiyar Afirka, za su fara cinikayyar hannayen jari, da takardun lamuni tsakanin su.

Da yake bayyana hakan a jiya Laraba, shugaban kasuwar cinikayyar hannayen jari ta Nairobin kasar Kenya Geoffrey Odundo, ya shaidawa manema labarai cewa, a yanzu haka akwai kasuwannin hannayen jarin kasashen Afirka 10, dake gwajin wannan tsari ta yanar gizo.

Mr. Odundo ya kara da cewa, masu hada-hadar hannayen jarin da za a shiga a dama da su a saye da sayarwar, sun hada da na kasashen Masar, da Ghana, da Botswana, da Kenya, da Najeriya da kasar Morocco. (Saminu)