logo

HAUSA

Karin Kamfanoni Za Su Halarci Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su Na Kasa Da Kasa Na Kasar Sin

2022-07-07 20:13:43 CMG Hausa

Karin kamfanoni za su halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake amfani da su na kasa da kasa karo na 2 da za a yi a birnin Haikou, babban birnin lardin Hainan na kudancin kasar Sin, daga 26 zuwa 30 ga watan Yuli.

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin, Shu Jueting ce ta bayyana haka yau Alhamis, inda ta ce adadin kamfanonin da za su halarci baje kolin a bana, ya zarce na bara, inda wurin baje hajoji zai karu zuwa muraba’in mita 100,000 daga 80,000. Kana sama da masu sayayya 40,000 ne aka sa ran za su halarci bikin.

Haka zalika, ta ce wurin baje hajoji na kamfanonin ketare zai karu da kaso 80 daga kaso 75 da ya kasance a bara.

A cewar kakakin, ta hanyar karbar bakuncin shirye-shirye tallata kayayyaki kamar na baje kolin, Sin na da burin gaggauta farfadowa da dorewar kasuwar sayen kayayyaki ta cikin gida, tare da ba bangaren damar taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. (Fa’iza Mustapha)