logo

HAUSA

Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo da Rwanda sun cimma matsayar dakatar da takun-saka

2022-07-07 15:03:24 CMG Hausa

Shugaban Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo Felix Tshisekedi, da takwaransa na Rwanda Paul Kagame, sun amince da fara aiwatar da matakan dakatar da takun-saka, bayan da sake bullar mayakan ’yan tawayen M23 ya haifar da zaman dar dar tsakanin kasashen biyu.

Shugabannin 2 sun cimma matsayar ne da tallafin mai shiga tsakani, kana shugaban kasar Angola Joao Lourenco, yayin zaman da ya gudana a birnin Luanda, fadar mulkin kasar Angola, bisa umarnin kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Tun karshen watan Maris, kungiyar ’yan tawayen M23, ta fara kaddamar da hare-hare a lardin Kivu ta Arewa dake gabashin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, lamarin da ya raba dubban fararen hula da gidajen su.

Daga bisani kuma, mahukuntan Jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, sun zargi kasar Rwanda da taimakawa ’yan tawayen a asirce, da niyyar haifar da rudani a yankin gabashin ta, zargin da gwamnatin Rwanda ta musanta.  (Saminu)