logo

HAUSA

Xi ya aikewa takwaransa na Aljeriya sakon murnar cika shekaru 60 da samun nasarar ‘yancin kasar

2022-07-05 14:31:27 CMG Hausa

Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa takwaransa na kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune, sakon murnar cika shekaru 60 da samun ‘yancin kan Aljeriya.

Cikin sakonsa, Xi ya yi nuni da cewa, kafin shekaru 60 da suka gabata, al’ummun Aljeriya sun yi gwagwarmaya, sun cimma burin samun ‘yancin kan kasar, kuma ya kasance zumunci mai zurfi tsakanin kasashen biyu wato Sin da Aljeirya, musamman ma a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, fahimtar juna a bangaren siyasa tsakanin kasashen biyu ya kara zurfafa a kai a kai.

Xi ya kara da cewa, yana mai da hankali matuka kan huldar dake tsakanin Sin da kasar Aljeriya, yana kuma fatan yin kokari tare da shugaba Tebboune, domin ingiza hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, bisa shawarar ziri daya da hanya daya. (Jamila)