logo

HAUSA

Manyan jami’an Sin da Amurka sun zanta ta kafar bidiyo

2022-07-05 10:33:05 CMG Hausa

Da sanyin safiyar Talatar nan ne mataimakin firaministan kasar Sin, kana mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kuma jagoran tawagogin kasashen Sin da Amurka game da hadaddiyar tattaunawar tattalin arziki Liu He, ya zanta ta kafar bidiyo da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen, bisa gayyatar sakatariyar.

Yayin zantawar tasu, sassan 2 sun yi musaya mai ma’ana, game da batutuwan da suka jibanci yanayin gudanar da hada hadar tattalin arziki, da samar da daidaito a fannin sarrafa hajojin masana’antu da shigar su kasuwanni. 

Har ila yau, sassan 2 sun amince cewa tattalin arzikin duniya na fuskantar mummunan kalubale, don haka nauyi ne a kan sassan 2, su karfafa tattaunawa kan manufofinsu na gudanar da tattalin arziki da tsare-tsare. 

Kazalika, ya kamata su yi aiki tare wajen wanzar da daidaito a fannin sarrafa hajojin masana’antu da shigarsu kasuwanni, ganin cewa hakan moriya ce gare su, da ma sauran kasashen duniya baki daya. 

Bugu da kari, bangaren kasar Sin ya nuna damuwa kan wasu batutuwa, da suka kunshi neman dage karin haraji kan hajojin kasar dake shiga Amurka, wanda gwamnatin Amurkan ta kakkabawa kamfanonin Sin, tare da fatan kyautata yanayin gudanar da harkoki ga kamfanonin na kasar Sin.   (Saminu Hassan)