logo

HAUSA

Mataimakin firaministan kasar Sin ya jaddada muhimmancin wanzar da nasarorin yaki da fatara

2022-07-05 11:01:59 CMG Hausa

Mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua, ya jaddada muhimmancin wanzar da nasarorin yaki da fatara, tare da bukatar ingiza raya yankunan karkara daga dukkanin fannoni, domin tabbatar da cewa, akasarin al’ummun da aka tsame daga kangin talauci ba su sake komawa ba.

Hu, wanda mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, ya yi wannan tsokaci ne, yayin ziyarar aiki da ya gudanar a jihar Tibet mai cin gashin kanta tsakanin ranekun 1 zuwa 4 ga watan nan na Yuli.

Mataimakin firaministan ya ganewa idanunsa yadda al’amura ke gudana a fannonin ayyukan yi, da sakamkon fitar da al’umma daga kangin talauci, da ci gaban noma mai halayyar musamman ta yankin, da ayyukan samar da ababen more rayuwa a kauyuka, da sauran hidimomin kyautata rayuwar al’umma da ake gudanarwa a jihar.

Hu ya ce ya kamata karfafa matakan yaki da fatara su zamo kan gaba a dukkanin sassa da aka cimma nasarori, don haka ya yi kira da a ci gaba da kara azama, wajen samar da damar kara kudaden shigar al’umma, ta hanyar inganta noma da kiwon dabbobi, da bunkasa sarrafawa, da yada amfanin gona zuwa kasuwanni, da fadada sashen yawon bude ido na kauyuka da dai sauran su. (Saminu)