logo

HAUSA

Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Dandalin Tattaunawar Masana Da Kafofin Watsa Labarai Game Da Tunanin Ci Gaban Duniya

2022-07-04 22:00:52 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron dandalin tattaunawar masana da kafofin yada labaru kan nazarin "raya duniya: manufar bai daya da kyawawan ayyuka".

Shugaba Xi ya jaddada cewa, a halin yanzu, duniya na fuskantar sauye-sauye da aka dade ba a ga irinsu ba, da kuma fama da bala'o'i, farfadowar tattalin arzikin duniya tana fama da rauni, gibin ci gaba tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu sukuni yana kara fadada, a hannu guda kuma duniya ta shiga wani sabon yanayi na tashin hankali da sauyi. Bunkasa ci gaban duniya ya zama babban aiki da daukacin bil- Adam ke fuskanta. Wannan ya sa, kasar Sin ta gabatar da shawarar raya kasashen duniya, a shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da dukkan kasashen duniya, da mayar da jama'a a gaban komai, da kiyaye hada kai, da samun bunkasuwa ta hanyar kirkire-kirkire, da daidaito tsakanin mutum da yanayi, da sa kaimi ga mayar da ci gaban kasashen duniya a gaban kome, don hanzarta aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030, a kokarin bunkasa ci gaban duniya na karin karfi, da kiyaye muhalli da lafiya. (Ibrahim)