logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Karbi Bakuncin Taruka Da Shirye-shiryen BRICS Kimanin 80 A Cikin Watanni Shida Na Karshen Bana

2022-07-04 20:35:57 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa Litinin din nan cewa, an kammala taron shugabannin kasashen BRICS cikin nasara, duk da cewa, an ci rabin shekara cikin “shekarar kasar Sin” ta BRICS, amma shugabancin kasar Sin na BRICS, zai ci gaba da tafiya cikin kyakkyaawan tsari.

Kasar Sin na shirin karbar bakuncin taruka da shirye-shirye kusan 80 a watanni shida na karshen wannan shekara. Kasar Sin na fatan yin aiki tare da sauran bangarori na BRICS, wajen aiwatar da sakamako, da matsaya daya da aka cimma yayin taron kolin BRICS, da kara karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da zurfafa hadin gwiwa a aikace a dukkan sassa, da karfafa kungiyar, ta yadda za a sa kaimi ga samun ci gaban kungiyar BRICS mai inganci.(Ibrahim)