logo

HAUSA

Sin: Bangaren Amurka Ne Ke Yada Labaran Bogi Da Karairayi

2022-07-04 20:20:26 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya musanta kalaman da jakadan Amurka dake kasar Sin R.Nicholas Burns ya yi game da rikicin kasashen Rasha da Ukraine da kuma dakin gwajin kwayoyin halittu na kasar Amurka dake Ukraine, yana mai jaddada cewa, jami'an Amurka ne, ba kasar Sin ba, wadanda suka rika yada labaran bogi da kuma yada karairayi.

Zhao Lijian ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana yanke hukunci bisa gaskiya da adalci ta hanyar dogaro da shaidu na tarihi da ‘yanci kan batun Ukraine.

Akwai bayanai masu tarin yawa da hujjoji game da batun dakunan gwaje-gwajin nazarin kwayoyin halittu na Amurka dake ketare, ciki har da kafa guda daya a kasar Ukraine. Al’ummomin kasa da kasa sun damu matuka game da wannan batu, kuma kasar Amurka na da alhakin yi wa duniya karin bayani.(Ibrahim)