logo

HAUSA

Hong Kong: An Bude Dakin Adana Kayan Tarihi Na Fadar Sarakuna Ga Al’umma

2022-07-03 21:02:04 CMG Hausa

A yau Lahadi an bude dakin adana kayan tarihi na fadar sarakuna ga al’umma a shiyyar al’adu ta West Kowloon, dake yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Sama da kayayyakin tarihi 900 da aka nuna, aka samo su ne daga fadar sarakuna wato Palace Museum dake Beijing, wadanda wasu daga cikinsu aka nuna su ne a Hong Kong a karon farko.

An sayar da kusan kashi 80 bisa kashi 100 na dukkan tikitoci 140,000 na shiga dakin adana kayan tarihin cikin makonni hudun farko da budewarsa.

Kevin Yeung, sakataren hukumar raya al’adu, wasanni, da yawon bude ido na gwamnatin Hong Kong na kasar Sin, ya ce dakin adana kayan tarihi na fadar sarakuna zai kara yin amfani da fifikon da Hong Kong yake da shi ta fuskar al’adu wajen bayyana kyakkyawan tarihin kasar Sin yadda ya kamata. (Ahmad)