logo

HAUSA

Shugaba Xi ya gana da jagoran yankin Hong Kong

2022-07-01 16:25:27 CMG HAUSA

 

Da safiyar yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sabon jami’in farko na hukumar gudanarwar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin (HKSAR) John Lee, inda ya bayyana cikakken goyon bayansa ga babban jami'in gudanarwar da kuma tabbaci game da makomar yankin Hong Kong.

Shugaba Xi ya bayyana yayin ganawa da babban jagoran yankin da aka rantsar a yau da safe cewa, mahukuntan gwamnatin tsakiya, za su baiwa John Lee da sabuwar gwamnatin yankin musamman na Hong Kong cikakken goyon bayan, wajen tafiyar da harkokin mulki bisa doka. (Ibrahim)