logo

HAUSA

Shugaba Xi ya gana da babbar kamtomar yankin musamman na Hong Kong

2022-06-30 19:58:37 CMG Hausa

A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da babbar kamtomar yankin musamman na Hong Kong Carrie Lam, inda ya bayyana cewa, gwamnatin tsakiyar kasar Sin, na sane da irin kokarin da ta yi cikin shekaru 5 da ta yi tana jagorancin Hong Kong.

Xi ya isa Hong Kong ne domin halartar bikin cikar yankin shekaru 25, da komawa karkashin ikon kasar Sin.

Shugaba Xi ya ce da cikakken goyon bayan gwamnatin tsakiya, Lam ta sauke nauyin dake wuyan ta, ta kuma aiwatar da tsarin “Kasa daya amma tsarin mulki iri biyu", da kuma dukkanin manufofin gudanarwar yankin na Hong Kong cikin shekaru 5 da suka gabata.

Ya kara da cewa, Lam ta jagoranci gwamnatin yankin musamman na Hong Kong wajen aiwatar da harkokin gwamnati bisa doka, da hade kan daukacin al’ummar yankin, ta yadda aka kai ga shawo kan tashin hankali, da dawo da yanayin zaman lafiya da oda a Hong Kong, kana an cimma nasarar yaki da annobar COVID-19, da hade yankin cikin manufofin ci gaban kasar baki daya.

Har ila yau, Lam ta yi aiki tukuru wajen ba da gudumawar kare ikon kasa, da moriyar ci gaba, da tabbatar da yanayin wadata da daidaito a Hong Kong. Kana ta aiwatar da ka’idojin masu kishin kasa su jagoranci Hong Kong, ta sharewa Hong Kong turbar sauya yanayi daga hargitsi zuwa zaman lafiya.

Xi ya kuma yi fatan ganin babbar kamtomar ta Hong Kong za ta ci gaba da tallafawa sabon kamtoman yankin, ta yadda zai cimma nasarar gudanar da gwamnati bisa doka.

A nata bangare, Lam ta godewa shugaba Xi bisa ziyarar da ya kai Hong Kong, yayin da ake tsaka da fuskantar kalubalen cutar COVID-19, tana mai cewa, matakin na sa ya nuna kulawar sa ga ‘yan uwa al’ummar Hong Kong.