logo

HAUSA

Rahoto: An samu yawaitar harbe dalibai a makarantun Amurka mafi muni cikin shekaru 20

2022-06-29 10:27:28 CMG Hausa

Sabon rahoton da aka fitar a ranar Talata ya nuna cewa, harbe-harben dalibai a makarantun kasar Amurka tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021, ya karu zuwa adadi mafi muni a cikin shekaru 20 da suka gabata.

An samu jimillar harbe-harbe a makaratun kasar 93 wanda ya yi sanadiyyar kashe dalibai a makarantun gwamnati, da masu zaman kansu, wanda ya kunshi makarantun firamare da na sakandare a shekarar karatun da ta gabata, wanda ya hada da harbe-harbe a makarantu kimanin 43 inda aka kashe dalibai, da kuma harbe-harbe a makarantu kimanin 50 wadanda suka jikkata dalibai ba tare da kisa ba, kamar yadda rahoton mai shafi 31 ya bayyana, wanda cibiyar kididdigar ilmi ta NCES, dake karkashin ma’aikatar kula da ilmi ta Amurka da cibiyar nazarin makarantun kimiyya ta Amurka suka wallafa.

Harbe-harben a makarantu na baya bayan nan da ya faru shi ne mafi muni a tarihin harbe-harbe a makarantun kasar. Kawo yanzu, sama da mutane 21,500 ne suka mutu a sakamakon harbe-harben bindiga a duk fadin Amurka a bana, kamar yadda alkaluman kididdigar harbe-harben bindiga na baya bayan wanda wata kungiya mai zaman kanta dake bin diddigin hare-haren da suka shafi harbin bindiga a kasar Amurka ta bayyana. (Ahmad)