logo

HAUSA

Sin ta shirya tarukan manema labarai da dama mai taken “Wadanan shekaru goma na kasar Sin”

2022-06-28 14:12:13 CMG HAUSA

 

A yau Talata 28 ga watan Yuni, sashen kula da harkokin yada labarai na kasar Sin ya gudanar da tarukan manema labarai daban-daban mai taken “Shekaru goma na kasar Sin". A wajen taron, an gabatar da cewa shirin samar da hatsi na kasar Sin ya samu bunkasuwa da sama da kilogram triliyan 1.3 a cikin shekaru bakwai a jere da suka gabata, lamarin da ya baiwa kasar zarafin samun wadatar hatsi kana an samu wadatar abincin da kasar ke bukata. A shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta samu nasarar daga matsayin dukkan fanni na bude kofar tattalin arzikinta, kana kasar ta cimma manyan nasarori a karkashin shirin hadin gwiwa na “ziri daya da hanya daya". Sama da daftarin hadin gwiwa 200 dake shafar shawarar “ziri daya da hanya daya” da aka daddale tare da sanya hannu daga kasashen duniya 149 da kuma kungiyoyin kasa da kasa 32. Bugu da kari, shirin yaki da talauci na kasar Sin ya samu gagarumar nasara, sannan dukkan mutanen dake fama da talauci dake yankunan karkarar kasa su miliyan 98.99, a halin yanzu an tsame su daga kangin talauci, lamarin da ya kasance wani abin al’ajabi a tarihin yaki da fatara na dan Adam. Haka zalika, shirin wayewar kai na kula da aikin gina muhallin halittu ya cimma muhimman sakamako. Manufar “dabarun farfado da ruwan tafkuna da yankunan masu tsaunuka arziki ne da ba za a iya kimanta darajarsu ba." Aikin ya yi matukar tasiri a zukatan al’umma, kuma jimillar makamashin da ake konawa kan kowane ma’aunin GDP ya ragu da kusan kashi 26.2% bisa 100. (Ahmad Fagam)