logo

HAUSA

Kashi na farko na kayayyakin agajin girgizar kasa da gwamnatin kasar Sin ta taimaka sun isa birnin Kabul

2022-06-28 10:15:08 CMG Hausa

Jiya ne, kashi na farko na kayayyakin agajin girgizar kasa da gwamnatin kasar Sin ta taimakawa Afganistan suka isa filin tashi da saukar jiragen sama na Kabul, babban birnin kasar Afganistan. Jakadan kasar Sin dake Afghanistan Wang Yu, da Gholam Gaus, mukaddashin ministan kula da bala'o'i da ayyukan jin kai na gwamnatin wucin gadin kasar Afghanistan, sun halarci bikin mika kayayyakin.

A jawabinsa jakada Wang Yu ya bayyana a yayin bikin mika kayayyakin cewa, girgizar kasar da ta afkawa kasar Afganistan, ta taba zukatan jama'ar kasar Sin, kuma nan take gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar ba da taimakon jin kai na gaggawa da darajarsa ta kai Yuan miliyan 50 ga yankin da bala'in ya shafa. A cikin kwanaki uku masu zuwa, jiragen sama na kasar Sin guda 6, za su ci gaba da kai kayayyakin agaji. Haka kuma, dukkanin kayayyakin abinci da kasar Sin ta yi alkawarin taimakawa Afghanistan, sun riga sun isa tun ‘yan kwanakin da suka gabata, kuma yanzu haka, an kara saurin rarraba kayayyakin abinci.

A nasa bangaren Gholam Gaus ya bayyana cewa, abubuwa da kasar Sin ta yi, yana nuna irin kyakkyawan zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu na tsawon dubban shekaru.(Ibrahim)